dc.description.abstract |
Wannan aiki mai suna “Kevavvun Kalmomin Intanet Da Amfaninsu A
Nazarin Hausa”, aiki ne da ya duqufa wajen samar da wani vangare na
kevavvun kalmomin intanet na Hausa. Da farko, aikin ya yi qoqari wajen
samar da kevavvun kalmomin intanet na Hausa ta hanyar fassara daga
Ingilishi zuwa Hausa. An yi nazarin kevavvun kalmomin da aka samar
qarqashin ilimin nahawun Hausa. Sannan aka yi gwajinsu a kan wasu
muhimman hanyoyi waxanda ake ganin samuwar kevavvun kalmomin intanet
na Hausa zai taimaka wa Hausa wajen amfani da intanet ba tare da bambancin
ma’ana ba. Babbar manufar wannan aiki ita ce ba da ‘yar gudummuwa wajen
bunqasa harkokin sadarwa na intanet a Hausa. Kodayake Hausawa sun daxe
da qwarewa a sha’anin sadarwa ta yau da kullum, amma sha’anin intanet a
yau ya riga ya shiga gaban kowace hanya ta sadarwa a wannan zamani.
Saboda haka dole ne Hausawa su qara qoqari wajen koyon kwamfuta da
amfani da intanet. A kan haka ne wannan bincike ya kammala da cewa Hausa
tana da haske a sha’anin intanet, domin gudummuwar da masana suka bayar a
vangaren hanyoyin sadarwa na kwamfuta sun nuna cewa Hausa tana da
kyakkyawar safiya. Sai dai, matuqar ana son wannan harshe ya ci gaba da
haskakawa, dole masana su taskace sababbin kalmomi na sha’anin kwamfuta
da intanet da kuma sauran vangarorin da ci gaban zamani ya kawo. Sannan
kuma Hausawa su shiga a dama da su a kowane vangare na amfani da
kwamfuta da intanet; sannan masu hannu da shuni da ‘yan kasuwa su saka jari
mai guivi a sha’anin sadarwa ta intanet. |
en_US |